Skip Global Navigation to Main Content
Search
 
 •  
 • Photo

  (copy)

 • #

  (copy)

 • Photo

  (copy)

 • Photo

  (copy)

 • Photo

  (copy)

Ko ina ka duba, zaka ga dalilan hana aiyukkan ta’addanci zagaye da kai

Akidar ta’addanci kan janyo asarar rayukka a ko ina. Bada bayani akan aiyukkan ta’addanci zai ceci dimbin rayukka, ya kare iyalai, ya sa a zauna lafiya.

 

Amurka na tayin bada lada mai tsoka ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga a kama masu aikata laifin ta’addanci. In kana da irin wannan bayanin, ka kawo shi yanzu-yanzu, bada bata lokaci ba.

 

Bada Bayani

Skip Breadcrumb Navigation

Labarai da Dumi-Duminsu

 • Muhammad al-Jawlani

  Muhammad al-Jawlani

  Har zuwa Ladan Dala Miliyan 10

  Muhammad al-Jawlani, wanda kuma aka sani da Muhammad al-Golani, wanda kuma aka sani da Muhammad al-Julani, babban jagora ne na ƙungiyar ta’addanci, wato al-Nusrah Front (ANF), reshen Syria na al-Qa’ida. A watan Aprilu, al-Jawlani ya yi mubaya’a ga al-Qa’ida da kuma jagoranta Ayman al-Zawahiri. A watan Yuli 2016, al-Jawlani ya yabawa al-Qa’ida da al-Zawahiri a wani faifan bidiyo na yanar gizo kuma ya yi iƙirari cewa ANF zata canza sunanta zuwa Jabhat Fath Al Sham (“Kame Filayen Daga”). A ƙarƙashin jagorancin al-Jawlani, ANF ta ƙaddamar da jerin hare-haren ta’addanci a Syria, wasu lokuta da suke harar fararen hula. A watan Aprilu na 2015, an bayar da rahoton cewa ANF ta sace mutane, kuma daga bisani ta saki a ƙalla fararan hula Ƙurdawa 300 daga wani wurin duba abuben hawa a Syria. A watan Yuni 2015, ANF ta ɗauki alhakin hallaka mutane 20 mazauna ƙauyen Druze na Qalb Lawzeh a gundumar Idlib, Syria. (Cikakken Bayani »)

 • Hoton Kisan Joel Wesley Shrum

  Kisan Joel Wesley Shrum

  Taizz, Yemen | 18 ga watan Maris, 2012

  A ranar 18 ga watan Maris, 2012, Shrum, mai shekaru 29, aka harbe shi kuma aka kashe shi a kan hanyarsa ta zuwa aiki a Taizz, Yemen, wanda wani ɗan bindiga da ke kan babur ya tsaya kusa da abin hawansa ya aikata. A lokacin rasuwarsa, Shrum yana aiki a Cibiyar Horo da Ci gaba Ta ƙasa-da-ƙasa a matsayin jami’i kuma malamin Turanci. Yana zaune a Yemen tare da matarsa da ƙananan yara guda biyu. Kwanaki kaɗan bayan harin, ƙungiyar ta’addanci ta al-Qaida dake Shashin Larabawa (AQAP) ta yi iƙirarin ɗaukan alhakin kisan. (Cikakken Bayani »)

 • Hoton Abu Du'a

  Abu Bakr al-Baghdadi

  Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 25

  Abu Bakr al-Baghdadi, wanda har wa yau aka san shi da lakabin Abu Du'a, da kuma lakabin Ibrahim ‘Awwad Ibrahim ‘Ali al-Badri, shine babban shugaban kungiyar ta’addanci ta Isalama ta Iraq da Levant (ISIL). Barazanar al-Baghdadi ta dada karuwa tun daga shekarar 2011, lokacin da Ma’aikatar Harakokin Waje tayi sanarwar bada goron Dala Milyan 10 ga duk wanda ya bada bayanin da ya kai ga inda yake, kama shi ko kuma kai ga yanke mishi hukunci. A cikin watan Yunin 2014 ne kungiyar ISIL, (wacce kuma aka sani da sunan Da’esh) ta kama sassa daban-daban a kasashen Syria da Iraq, ta girka mulkin Islamiyya kuma ta nada al-Baghdadi a matsayin shugaban addini na wuraren. A shekarun da suka gabata, ISIL ta sami mubayi’ar kungiyoyin ‘yan jihadi da dama da kuma nasarar cusawa mutane akidar addini mai tsanani a kasashen duniya daban-daban, ta kuma karfafa gwiwar a rinka kai hare-hare akan Amurka. (Cikakken Bayani »)

 • Gulmurod Khalimov

  Gulmurod Khalimov

  Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

  Tsohon Kanar na Sojan Tajikistan, kwamandan ‘yansanda, gwanin harbi na soja, Gulmurod Khalimov, jami’in Kungiyar ‘yan Islama ta ISIL ta Iraq da Levant ne kuma mai daukar mata ma’aikata. Shi ne babban kwamnadan wata bataliyar soja ta musamman da aka kafa a cikin Ma’aikatar Harakokin Cikin Gida ta Tajikistan. Khalimov ya taba fitowa cikin wani faifan bidiyon farfaganda da aka yi, inda aka ganshi yana tabattarda cewa lalle shi mayakin ISIL ne kuma har, a bainar jama’a, yana kira ga a kai wa Amurkawa farmaki na ta’addanci. (Cikakken Bayani »)

 • Hoton Abu-Muhammad al-Shimali

  Abu-Muhammad al-Shimali

  Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

  Tun cikin shekarar 2005 ake alakanta Tirad al-Jarba da aka fi sani da lakabin Abu-Muhammad al-Shimali, wanda kuma shine Shugaban Harakokin Kan Iyakoki na Kungiyar Al’ummar Islama ta Iraq da Levant (ISIL) da ita kungiyar ta ISIL, wacce a can da aka sani da sunan al-Qaida a Iraq. Yanzu haka shine yake jagorancin aiyukkan da suka danganci Shige da Fice da kuma Samarda Kayan Aikin (Cikakken Bayani »)

 • Hoton Fasa-Kwabrin Kayan Tarihi da na Mai dake anfanar Kungiyar Islama ta Iraq da Levant (ISIL)

  Fasa-Kwabrin Kayan Tarihi da na Mai dake anfanar Kungiyar Islama ta Iraq da Levant (ISIL)

  Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada ladar da zata kai har Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga tsaida saye ko sayarda mai da kayan tarihi da ake don anfani, ko da sunan, ko a madadin kungiyar ‘yan ta’addar nan ta ‘yan kishin Islama (ISIL) ta Iraq da Levant wacce kuma aka sani da lakabinta na Larabci, watau DAESH. (Cikakken Bayani »)

Labarai Kan Nasarorin Da Aka Samu

Hoton Ramzi Ahmed Yousef

Wanda aka yanke wa hukunci

Bayanin da ya sa aka kai ga yanke wa Ramzi Ahmed Yousef hukunci

Ramzi Yousef ne ummulhaba’isun shirya harin bam da aka kai kan Cibiyar Ciniki ta Duniya a watan Fabrairun 1993 a birnin New York, harin da ya hallaka mutane shidda, ya raunana fiyeda mutane dubu daya.Yousef da mukarabbansa sun tuka motar da aka shake da bama-bammai ne zuwa karkashin Cibiyar Ciniki. Sa’oi kalilan bayan kai harin, Yousef ya arce zuwa Pakistan ta cikin jirgin sama.

Daga baya ne Yousef ya bulla akasar Philippines inda ya shiga cikin wani sabon makirci na ta’addanci. Yousef ya shirya kashe Paparoma John Paul II... (Cikakken Bayani »)

Muyi cudanya


twitter   facebook   youtube   rss